Bangaren al'adu da zamantakewa; Iraniyawa mazauna kasar Serbia sun gudanar da taron maulidin Imam Mahdi (AS) a mazaunin jakadan kasar Iran da ke birnin Belgarad fadar mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren hulda da jama'a na cibiyar kula da harkokin al'adu da bunkasa a ilimi ta Iran ya bayyana cewa, Iraniyawa mazauna kasar Serbia sun gudanar da taron maulidin Imam Mahdi (AS) a mazaunin jakadan kasar Iran da ke birnin Belgarad fadar mulkin kasar ta Serbia.
A lokacin gudanar da taron maulidin an gabatar da bayanai kan matsayin ranar a addinin musulunci gami da falalar da ke tattare da ita, bugu da kari kuma da babban matsayin da take Bantu da shi na haihuwar Imam Mahdi (AS) a cikinta
Jakadan Iran da sauran malaman da suka halarci taron maulidin sun e suka gabatar da jawaban, haka nan kuma an shirya walima bayan kamala sauraron bayanai.
621684