IQNA

Za A Gudanar Da Taron Dangantakar Tarihi Tsakanin Iran Da Turkiya

Bangaren al'adu da fasaha; Shugaban ofishin cibiyar bunkasa harkokin ilmi da al'adu ta Iran a reshenta na kasar Turkiya ya bayyana cewa za a gudanar da wani zaman taro kan dangantakar tarihi tsakanin kasashen Iran da Turkiya a cikin 'yan watanni masu zuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban ofishin cibiyar bunkasa harkokin ilmi da al'adu ta Iran a reshenta na kasar Turkiya ya bayyana cewa za a gudanar da wani zaman taro kan dangantakar tarihi tsakanin kasashen Iran da Turkiya a cikin 'yan watanni masu zuwa a nan gaba akasar ta Turkiya.

Ya ci gaba da cewa kasashen Turkiya da Iran kasashe ne masu dadadden tarihi da babu wani mahaluki da zai iya raba kasashen biyu, kuma za su ci gaba da bunkasa dangantaka ta ilimi a tsakaninsu da musayar al'adu.

621606