IQNA

Karkata Zuwa Ga Duniya Ta Banbata Mahangar Turai Da Mahdawiya

13:43 - July 28, 2010
Lambar Labari: 1963301
Bangaren kasa da kasa; Karkata zuwa ga duniya cikin dukkanin lamurra shi ne babban abin da ya banbanta mahangar turai kan gyara makomar duniya da kuma akidar mahdawiyya da musulmi suke da ita.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da daya daga cikin mahalarta taron mahdawiyya da ake gudanarwa a jamhuriyar musulunci ta Iran daga kasar Morocco Nuruzeh Ahmad ya bayyana cewa, karkata zuwa ga duniya cikin dukkanin lamurra shi ne babban abin da ya banbanta mahangar turai kan gyara makomar duniya da kuma akidar mahdawiyya da musulmi suke da ita a cikin addininsu.

Ya ci gaba da cewa musulmi sun yi imanin cewa komai yadda lamurra suka bace akwai mai gyara yana zuwa daga Allah, kuma gyaran da zai yi tare yake da isar da sakon ubangiji tare da shiyar dad an adam zuwa ga sahihin tafarki na kadaita Allah a cikin bauta, tare da jadda sakon manzon Allah (SAW) ga al'ummar duniya.

Ya yin da su kuma yammacin turai suna tunanin za a yi gyara ne kawai saboda duniya, kuma babbar manufar gyaran da suke tsammanin za a yi saboda duniya ne.

622103


captcha