Bangaren kasa da kasa; Limamin masallacin Najaf Ashraf Sayyid Sadruddini Kubanci ya bayyana cewa, horar da matasa da ake yi kan ilmomin kur'ani mai tsarki na da matukar muhimmanci a rayuwar al'umma ta zamantakewa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na alqubanci.com an habarta cewa, limamin masallacin Najaf Ashraf Sayyid Sadruddini Kubanci ya bayyana cewa, horar da matasa da ake yi kan ilmomin kur'ani mai tsarki na da matukar muhimmanci a rayuwar al'umma ta zamantakewa, tare da bayar da damar ilmantar da su hakikanin koyarwa ta iyalan gidan manzon Allah bisa mahangar kur'ani.
Ya kirayi malamai da masana a kasar da su mayar da hankali wajen fadada harkokin ilmantar da matasa kan ilmomin kur'ani mai tsarki.
Malamin ya jaddada cewa batun ilmantar da matasa ba aiki ne na wani bangare ba kawai, dole ne kowa kama daga iyaye, mahukunta masana kowa ya bayar da gudunmawarsa.
621972