IQNA

An Zabi Sabon Shugaban Kungiyar Jami'oin Musulunci

13:42 - July 28, 2010
Lambar Labari: 1963306
Bangaren kasa da kasa; An zabi sabon shugaban kungiyar hadakar jami'oin kasashen musulmi Sulaiman Bin Abdullah Aba khail, wanda zai ci gaba da rike matsayin har zuwa alokacin da za a sake gudanar da wani zaben.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na daya cikin manyan cibiyoyin Musulunci a shafin yanar gizo an bayyana cewa, an zabi sabon shugaban kungiyar hadakar jami'oin kasashen musulmi Sulaiman Bin Abdullah Aba khail, wanda zai ci gaba da rike matsayin har zuwa alokacin da za a sake gudanar da wani zaben irin wannan.

Bayanin ya kara da cewa kungiyar tana taka gagarumar wajen hada kan jami'oin kasashen musulmi, tare da daukar manhaja da ta yi daidai da yanayin kasashe.

622031



captcha