IQNA

A Gobe Za Bude Masallacin Sayyida Zahra (AS) A Garin Saihat

20:15 - July 28, 2010
Lambar Labari: 1963522
Bangaren kasa da kasa; A gobe idan Allah ya kai mu za a bude wani masallaci da aka baiwa suna masallacin Sayyida Zahra (AS) a garin Saihat da ke gabacin kasar Saudiyya, inda mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) suke fi yawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar sadarwa ta Rasid cewa, a gobe idan Allah ya kai mu za a bude wani masallaci da aka baiwa suna masallacin Sayyida Zahra (AS) a garin Saihat da ke gabacin kasar Saudiyya, inda mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) suke fi yawa a kasar.

Rahoton ya ce wannan masallaci mabiya mazhabar shi'a ne suka gina shi da kansu, kujma sun ba shi wannan suna na Sayyid Zahra, domin samun albarkar mai sunan.

621938




captcha