Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na Nun an bayyana cewa, mahukuntan birnin Karbala mai alfarma sun da hutu a hukumance saboda tarukan da ake gudanarwa a birnin na tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imam Mahdi (AS) wanda ya yi daidai da ranar sha biyar ga watan sha'aban da muke ciki.
Kakakin gwamnatin lardin Karbala Hassan Udai ya bayyana cewa an dauki wannan matakin ne sakamakon cunkoso da ake samu a lokacin gudanar dairin wadannan taruka masu albarka.
Ya ce an bayar da hutun domin samun albarkar ranar, da kuma bayar da dama ga mutane su gudanar da hidimominsu saboda baki da suke isowa birnin domin halartar tarukan.
621921