IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Kur'ani A garin Alfujaira Na UAE

20:15 - July 28, 2010
Lambar Labari: 1963524
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki a garin alfujaira na kasar hadaddiyar daular larabawa a cikin watan Ramadan mai zuwa, wanda cibiyar kula da bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta dauki nauyyin shiryawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar albayan da ake bugawa a kasar hadaddiyar daular larabawa ta habarta cewa za a gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki a garin alfujaira na kasar hadaddiyar daular larabawa a cikin watan Ramadan mai zuwa, wanda cibiyar kula da bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta birnin ta dauki nauyyin shiryawa da gudanarwa kamar yadda ta saba yi a kowace shekara.

Rahoton ya ce a lokacin gudanar da gasar za a samu halartar makaranta da mahardata da ma masana gami da malamai daga sassa daban-daban na kasar.

Yanzu haka dai an mika dukkanin shirye-shiryen da aka domin gudanar da gasar ga kwamitin kula da shirya gasar kur'ani na kasar hadaddiyar daular larabawa domin gudanar da gyare-gyaren da suka kamata.

621913



captcha