Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren yada labaransa na yankin Balkan ya habarta cewa, musulmin kasar Bosnia sun nuna rashin amincewa da dokar hana saka nikabi a kasar wadda wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar suka gabatar da daftarin kudiri da nufin tattaunawa kansa a zaman majalisar da ta saba gudanarwa.
Wannan daftarin kudiri dai yana yin nuni da cewa saka nikabi a wurare na jama'a yana da aibu matuka, domin kuwa zai iya zama baraza ga harkar tsaro, kamar yadda ya saba wa yanayi na zamantakewar jama'a.
A daidai lokacin da majalisar za ta gudanar da zaman tattauna daftarin kudirin wasu mata sun gudanar da zanga-zangar yin Allawadai da daftarin kudin.
622147