IQNA

Wata Mai Sheakaru 100 Ta Lashe Gasar Kur'ani A Saudiyya

21:22 - July 29, 2010
Lambar Labari: 1963737
Bangaren kasa da kasa; Wata mata 'yar shekaru 100 da haihuwa ta lashe gasar harda da karatun kur'ani ta mata da aka gudanar a lardin Basha'ir da ke kudancin kasar Saudiyya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga jaridar Ukaz da ake bugawa a kasar Saudiyya an habarta cewa, Wata mata 'yar shekaru 100 da haihuwa ta lashe gasar harda da karatun kur'ani ta mata da aka gudanar a lardin Basha'ir da ke kudancin kasar Saudiyya, wadda gasar ta kebanci mata makaranta kur'ani ne.

Matar wadda ta shiga gasar a bangaren harda ta karanta ba tare da wani kuskure ba, kamar yadda ta amsa dukkanin tambayoyin da aka yi mata kan harda da kuma ilmin tajwidi, inda shi ma ba yi kuskure ko daya ba.

622530



captcha