IQNA

Maulidin Imam Mahdi (AS) Na Da Muhimmanci Wajen Hada Kan Musulmi

21:21 - July 29, 2010
Lambar Labari: 1963741
Bangaren kasa da kasa; Sayyid Abul kasim Dibaji babban sakataren kwamitin fikihun musulunci na duniya,awakilin Ayatollah Sistani a kasar Kuwait ya bayyana cewa, gudanar da tarukan maulidin Imam Mahdi (AS) na cikin muhimman abubuwan da ke taimaka ma hadin kan musulmi.




Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto day a nakalto daga jaridar Alra'ay da ake bugawa a kasar Kuwait an habarta cewa, Sayyid Abul kasim Dibaji babban sakataren kwamitin fikihun musulunci na duniya, kum awakilin babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Ali Sistani a kasar Iraki ya bayyana cewa, gudanar da tarukan maulidin Imam Mahdi (AS) na da daga cikin muhimman abubuwan da ke taimaka ma hadin kan musulmi daga mazhabobi daban-daban.

Ya ci gaba da cewa irin yadda aka gudanar da tarukan bukin maulidin Imam Mahdi a wannan shekara ya tabbatar da cewa musulmi duka suna tsammanin mafita daga bayyanar ImamMahdi (AS)

622504




captcha