Bangaren kasa da kasa; An bude taron gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa akasar Malazia tare da halartar sarki kasar, inda makaranta daga kasashen Senegal, Morocco da kuma India suka bude gasar da karatun ayoyin kur'ani mai girma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, dan rahotonsa ya habarta cewa, an bude taron gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa akasar Malazia tare da halartar sarki kasar, inda makaranta daga kasashen Senegal, Morocco da kuma India suka bude gasar da karatun ayoyi daga kur'ani mai tsarki.
Wannan dai shi ne karo hamsin da biyu da ake gudanar da irin wannan gasar kur'ani ta kasa da kasa a kasar ta Malazia a kowace shekara a jeer, tare da halartar mahardata kur'ani gami da makaranta daga sassa daban-daban na kasashen duniya.
622251