Bangaren al'adu da fasaha; An bude wata bababr cibiyar kula da harkokin addinin musulunci mai suna albar islami a birnin Yala da ke kudancin kasar Thailand, wanda babban kwamitin kula da harkokin musulunci na kasar ya dauki nauiyin ginawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na yankin Asia ta tsakiya an habarta cewa, an bude wata bababr cibiyar kula da harkokin addinin musulunci mai suna albar islami a birnin Yala da ke kudancin kasar Thailand, wanda babban kwamitin kula da harkokin musulunci na kasar ya dauki nauiyin ginawa tare da gudanar da ayyuakanta.
Daga cikin abubuwan da wannan cibiya ta kunsa akwai babban dakin gudanar da taruka, gami da azuzuwan koyar da karatu, da dai sauran lamurra da suka danganci harkokin musulunci.
622638