Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a rahoton da ya nakalto daga dan rahotonsa na musamman daga dakin gudanar da gasar kur'ani ta Malazia ya bayyana cewa, makarantar kur'ani na kasar Iran da kuma kasar Qatar sun ja hankulan dukkanin mahalarta gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da ke gudana a kasar Malazia a birnin Kualampour.
Rahoton ya ci gaba da cewa dukkanin makarantan biyu sun gudanar da karatu mai jan hankali a dukkanin bangarori, da hakan ya hada yadda suke fitar sauti da kiyaye ka'idojin karatun.
Yanzu haka dai ana ci gaba da gudanar da wannan gasa tare da halartar daruruwan mahardata da makaranta daga kasashen musulmi da na larabawa, da wasu kasashen dab a na musulmi ba.
623438