Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, mai aiko masa labarai daga kasar Malazia ya habarta cewa, a rana ta hudu ta gasar karatun kur'ani mai tsarki a matsyi na kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia, makaranta da mahardata daga kasashen duniya na ci gaba da karawa da juna a wannan gasar.
Rahoton ya kara da cewa wannan gasa tana samun karbuwa daga dukkanin mahalarta da kuma masu sanya ido kan yadda take gudana.
Makaranta da daman e suka kara da juna yayin da ake a matsayi na fara tantancewar farko, daga bisani kuma za a shiga bangaren tantacewa ta tsakiya kafin shiga bangaren karshe.
623418