IQNA

Aikin Musulmi Ne Su Yada Tunanin Mahdawiyya A Duniya

17:28 - July 31, 2010
Lambar Labari: 1964580
Bangaren kasa da kasa; Dukkanin musulmi a ko'ina suke cikin fadin duniya suna da imanin cewa Mahdi zai bayyana domin kubutar da duniya daga karkkata tare da mayar da ita kan da'a ga Allah, saboda haka wajibi ne a kansu su yada wannan tunani a duniya.


A wata zantawa da ta hada kamfanin dillacin labaran iqna da Shanuvaz Ali Raihan daya daga cikin mambobin kwamitin kula da harkokin dalibai musulmi a kasar India ya bayyana cewa, dukkanin musulmi a ko'ina suke cikin fadin duniya suna da imanin cewa Mahdi zai bayyana domin kubutar da duniya daga halin karkkata tare da mayar da ita kan da'a ga Allah madaukakin sarki, saboda haka wajibi ne akansu su yada wannan tunani ga sauran al'ummomin duniya baki daya.

Ya kara da cewa kamar yadda musulmi suke da imani kan bayyanar mahdi haka sauran addinai suke da imanin cewa wani zai zo domin tsaeratar da duniya daga bala'in zalunci da ta samu kanta a ciki, tare da tabbatar da adalci, a kan haka akwai bukatr sauran al'ummomi su san mahangar musulmi kan mahdi.

623324
captcha