Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar Almadina da ke fitowa a kasar Saudiya ta watsa rahoton cewa; taron kasa da kasa na kungiyoyin musulmi na duniya za su gudanar a yau din tara ga watan Murdad na shekara ta dubu da dari uku da tamanin da tara shekara ta hijira shamsiya.Abdallah bin Abdulla Muhsin Alturki babban sakataren kungiyoyin addinin Musulunci dangane da wannan lamari ya bayyana cewa;an gayyaci malama da shehunan malamai a duniyar musulmi da shugabannin cibiyoyi da kungiyoyi na addinin Musulunci domin halartar wannan taro.
623277