IQNA

Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Ashbalul Kur'ani A Riyad

17:47 - July 31, 2010
Lambar Labari: 1964596
Bangaren kasa da kasa : masallacin Alfaruk da ke birnin Riyad babban birnin Saudiya za a gudanar da gasar Hardar Kur'ani mai girma ga yara kanana da aka bawa taken Ashbalul Kur'ani ma'ana Yaran Kur'ani.


Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar saudiya ta Iktisadiya ta watsa rahoton cewa; masallacin Alfaruk da ke birnin Riyad babban birnin Saudiya za a gudanar da gasar Hardar Kur'ani mai girma ga yara kanana da aka bawa taken Ashbalul Kur'ani ma'ana Yaran Kur'ani. Wanna karo wannan gasa za a gudanar da ita ne a ranar ashirin da tara ga watan Sha'aban da kuma za a ci gaba da gudanar da wannan gasa har zuwa ranar ashirin ga watan Ramadana na wannan shekara inda yara da dama za su fafata da junansu a wannan gasar harda ta kur'ani mai girma .

623249







captcha