IQNA

Ziyarar Qods Da Visa Ta Isra'ila Zuwa Ya Saba Wa Shari'a

17:54 - July 31, 2010
Lambar Labari: 1964601
Bangaren kasa da kasa; Yin tafiya zuwa birnin Qods mai alfarma tare da ziyartar masallaci mai malfarma da takardun izinin shiga na Isra'ila ya saba wa shari'a kuma yin hakan daidai yake da amincewa da halascin haramramtacciyar kasar Isra'ila.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran iba an bayyana cewa, babban malamin addini na kasar Kuwait ya bayyana cewa, Yin tafiya zuwa birnin Qods mai alfarma tare da ziyartar masallaci mai malfarma da takardun izinin shiga na Isra'ila ya saba wa shari'a kuma yin hakan daidai yake da amincewa da halascin haramramtacciyar kasar yahudawan sahyuniya.

Malamin ya kara da cewa ziyartar Qods na da babban muhimmanci, amma tare da izinin haramtacciyar kasar Isra'ila ya sabawa shari'a.

Y ace idan musulmi zasu iya halartar masallacin mai alfarma ba tare da takardun izinin shiga na Isra'ila ba to su ziyarce, idan kuma ba haka ba, ziyarar ta fadi a kansu, wadanda ke zaune a birnin sun isar musu.

623233
captcha