IQNA

Taro Kan Tattauna Hanyoyin Bunkasa Ayyukan Al'adu Da ISESCO

Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro tsakanin jami'an cibiyar bunkasa harkokin ilmi da al'adu da kuma kungiyar bunkasa ilimi da al'adu ta kasashen musulmi ISESCO kan hanyoyin da za a bi wajen kara bunkasa harkokin ilimi da ala'du na kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa, za a gudanar da wani zaman taro tsakanin jami'an cibiyar bunkasa harkokin ilmi da al'adu da kuma kungiyar bunkasa ilimi da al'adu ta kasashen musulmi ISESCO kan hanyoyin da za a bi wajen kara bunkasa harkokin ilimi da ala'du na kasashen musulmi na duniya.

Rahoton ya ce taron zai hada bangarori da daman a gwamnatin Iran da suka hada da ita kanta cibiyar bunkasa al'adu da ilimi ta Iran, gami da bangaren ma'aikatar harkokin wajen kasar, da kuma babbar cibiyar ahlul bait ta duniya.

Haka nan kuma taron zai samu halartar jami'ai daga ma'aikatar ilimi ta kasa, da kuma cibiyar kusanto da mazhabobin musulunci gami da jami'ar Almostafa, da kuma cibiyar kula da ayyukan haji da ziyara ta kasa.

Za a dai gudanar da zaman taron ne a birnin Qom tare da halartar daga dukkanin bangarorin da aka ambata, gami da wakilai da kungiyar ISESCO ta duniya.

623811