IQNA

Malaman Kuwait Sun Yi Allawadai Da Ayyana Ranar Kone Kur'ani

9:40 - August 01, 2010
Lambar Labari: 1964685
Bangaren kasa da kasa; Bayan fitar da bayani da wata majami'a ta yi a kasar Amurka da ke a sanya ranar kona kur'ani ta duniya, malaman kasar Kuwait gami da masanan kasar sun fitar da wani bayani da ke yin Allawadai da hakan.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alanba ta kasar Kuwait an habarta cewa, bayan fitar da bayani da wata majami'a ta yi a kasar Amurka da ke a sanya ranar kona kur'ani ta duniya, malaman kasar Kuwait gami da masanan kasar sun fitar da wani bayani da ke yin Allawadai da wannan sanarwa.

Rahoton ya ce a cikin bayanin da masanan suka fitar sun jadda cewa wannan wata tsokana ce ake nufin musulmi da ita, kuma ya zama wajibi kan dukkanin al'ummar musulmi da su mike tsaye domin tunkarar irin wannan mummunan aiki.

Jawabin ya ce ba ya rasa nasaba da irin matakan da ake gain a cikin 'yan lokutan nan da wasu masu tsananin kiyayya da musulunci suke dauka a cikin kasashen turai na muzanta ababe masu tsarki na addinin musulunci.

Daga cikin abubuwan da aka gain a lokutan baya hard a cin zarafin manzon Allah (SAW) da kuma shirya fim na wulakanta kur'ani da addinin musulunci, wanda duka hakan na bukatar mikewar musulmi a duniya baki daya.

623708
captcha