Bangaren kasa da kasa; Kauyen Imam Huseini (AS) da aka gina na musamman ga masu ziyarar Aba Abdullahi Huseini (AS) a marecen ranar takwas ga watan Murdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya aka bude shi a yankin Alfariha da ke tazarar kilomita biyar da gabacin Karbala.
Majid Naji mai magana da yawun kafar Nun bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta kusa da ofishin magajin garin karbala ya shaidawa cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna cewa; Kauyen Imam Huseini (AS) da aka gina na musamman ga masu ziyarar Aba Abdullahi Huseini (AS) a marecen ranar takwas ga watan Murdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya aka bude shi a yankin Alfariha da ke tazarar kilomita biyar da gabacin Karbala.Gina wannan kauye ko shakka babu zai taimakawa da kawo sauki ga masu ziyarar yankin Karbala'a musamman da ke fitowa daga kasashe daban daban ko yankuna daban daban na Iraki na kwarara a wannan yanki na Karbala.
623482