Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren kula da harkokin al'adu an bayyana cewa, wasu tashoshin talabijin da ke watsa shirye-shiryensu kan tauraron dan sun bayyana cewa za su fitar da wasu bayai da gami da hotuna na wasu masallatai wanda ake lissafa su a matsayin dadaddun masallatan Musulunci.
Daya daga cikin wadannan masallatai shi ne masallacin marigayi Imam Khomeini (RA) da ke birnin Esfahan, wanda aka gina tun lokacin mulkin sarakunan abbasiyawa a karni na uku, wanda bai gushe ba har inda yau take ana gudanar ayyukan ibada a cikinsa.
624312