Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wani labari daya nakalto daga kamfanin dillancin labaran saba na palastinu an habarta cewa, hukumar kwarya-kwaryan cin gishin kai ta palastinawa ta kirayi bangaren haramtacciyar kasar Isra'ila da ta dakatar da ayyukan wuce gona da irin da take aikatawa a cikin yankunan palastinawa da hakan ya hada da gina matsugunnan yahudawa 'yan kaka gida a cikin yankunan palastinawanm musamman ma mazauna gabacin birnin Qods.
Ya kara da cewa yanzu haka haramtacciyar kasar Isra'ila ta ci gaba da gudanar da ayyukan mamaya a cikin yankunan palastinawan, duk kuwa da kiraye-kirayen da al'ummomin duniya suke yi mata na ta dakatar da hakan.
624330