IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun Mamaye Kafofin Sadarwa Na Turai

17:46 - August 02, 2010
Lambar Labari: 1965972
Bangaren kasa da kasa; Rawar da cibiyoyin yahudawan sahyuniya ke takawa a cikin harkokin sadarwar kasashen turai dalili ne da ke tabbatar da cewa sun mamaye harkar sadarwa a kasashen turai da ke babatun 'yanci a dukkanin bangarorin rayuwar dan adam.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani labari daga shafin sadarwa na islamonline cewa, rawar da cibiyoyin yahudawan sahyuniya ke takawa a cikin harkokin sadarwar kasashen turai dalili ne da ke tabbatar da cewa sun mamaye harkar sadarwa a kasashen turai da ke babatun 'yanci a dukkanin bangarorin rayuwar dan adam a baki.

Wannan rahoto ya kara da cewa babban abin kunya da kafofin yada labarai na kasashen yammacin turai suke tafkawa, ya tabbatarwa duniya da cewa abin da suke fada da baki ba shi ne a cikin ayyukansu ba.

Daga cikin misalasai kan hakan kuwa har da yadda suke boye duk wani labari da ya shafi wata tabargaza da yahudawan sahyuniya suke tafkawa a kan al'ummar palastinu da ma sauran al'ummomin duniya.

624271


captcha