IQNA

Ana Bin Diddigin Rashin Samun Iraniyawa Cikin Alkalan Gasar Malazia

11:06 - August 04, 2010
Lambar Labari: 1966979
Bangaren kasa da kasa; Ana bin diddigin dalilan rashin samun iraniyawa a cikin alkalan gasar kur'ani mai tsaki ta kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Kualalampour na kasar Malazia.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi jakadan jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Malazia Muhammad Mahdi Zahidi ya bayyana cewa, ana bin diddigin dalilan rashin samun iraniyawa a cikin alkalan gasar kur'ani mai tsaki ta kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Kualalampour na kasar Malazia, da za a kammala a cikin mako mai zuwa.

Ya ci gaba da cewa gasar kur'ani ta kasa da kasa da ke gudana a kasar ta Malazia gasa mai matukar muhimmanci a matsayi na kasa da kasa, a kan haka yana da matukar muhimmanci ga Iran ta kasance kan gaba a cikin alkalancin gasar.

Dangane da batun halartar makaranta da mahardata iraniyawa a gasar ya bayyana cewa babu laifi sun yi rawar gani, kuma za su ci gaba da yin dubi kan dukkanin bangarorin halartar makarantan da kuma alkalan gasa.

625649




captcha