Bangaren kasa da kasa; An kammala gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki ta kasar Bolgaria, wadda babban kwamitin manyan malaman addinin Musulunci masu bayar da fatawa a kasar ya shirya gudanarwa a garin Kircaali.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na kircaali cewa, an kammala gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki ta kasar Bolgaria, wadda babban kwamitin manyan malaman addinin Musulunci masu bayar da fatawa a kasar ya shirya gudanarwa a garin Kircaali na kasar.
Babban mai bayar da fatawa na kasar Bolgaria Mustafa Haji ya bayyana cewa, gudanar da irin wannan gasa na da matukar muhimmanci wajen karfafa musulmin kasar domin ci gaba da mayar da hankali ga koyarwar kur'ani mai tsarki.
625695