Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Muhit an bayyana cewa, babban malamin jami'ar Azhar ta kasar Masar Ahmad Tayyib ya bayyana cewa wajibi ne a fara koyar da harshen farisanci a cibiyoyin da ke karkashin jami'ar a kasar Masar da ma sauraren rassanta.
Bayanin ya ci gaba da cewa bisa la'akari da cewa harshen fararisanci a cikin ala'du na mutanen yankin gabas ta tsakiya, da kuma rubuce-rubucen da aka yi da wannan harshe, za a saka shi cikin yarukan da za a rika koyarwa a jami'ar.
Ahmad Tayyib ya ce bugu da kari akwai yarukan turancin ingilishi, Faransanci, da Turkanci gami da harshen Hibru duk suna daga cikin manyan yaruka da suke da amfani ga daliban jami'ar, kuma duk akwai shirin koyar da su a nan gaba.
625867