Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Al-riyad da ake bugawa a kasar saudiyya cewa, babban kwamitin bincike da nazari na kasashen musulmi ya gudanar da wani zama a birnin Makka mai tsarki da nufin tattauna hanyoyin da za a bi wajen hanya ta gudanar da nazarin addinin Musulunci a dukkanin jami'oi na kasashen duniya musamman ma a kasshen turai.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro ya yi dubi kan wasu batutuwa na daban, da suka hada batun ci gaba da killace yankin zirin Gaza da haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da yi.
Taron ya bukaci da a dauki dukkanin matakan da suka dace na matsa lamba kan kan yahudawan sahyuniya da su janye takunkumin da suka kakaba ma al'ummar yankin.
625747