Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran saba na kasar yeman ya habarta a shafinsa na yanar gizo cewa, an gudanar da wani shiri na musamman kan wayar da kan mata musulmi dangane da hakkokin da mace ta ke da su a mahanga da dokoki na addinin Musulunci, wanda cibiyar kula da ayyukan mata ta kasar ta shirya gudanarwa a garin Abin.
Bayanin ya kara da cewa dukkanin matan da suke halartar wannan shiri suna wakiltar kungiyoyi ne daban-daban na mata musulmi a lardunan kasar, wadanda za su isar da dukkanin abubuwan da suka koya yayin zaman ga sauran 'yan uwansa.
625835