Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro da aka bai wa take makon kur'ani mai tsarki a birnin Karbala mai alfarma na kasar Iraki, wanda cibiyar raya ala'du da ilimin ta kasar Iran ta shirya gudanarwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da Mohsen pakayin shugaban bangaren bunkasa alaka da cibiyoyin addini na kasa da kasa ya bayyaan cewa, za a gudanar da wani zaman taro da aka bai wa take makon kur'ani mai tsarki a birnin Karbala mai alfarma na kasar Iraki, wanda cibiyar raya ala'du da ilimin ta kasar Iran ta shirya gudanarwa tare da hadin gwiwa da wasu cibiyoyin addini na kasar Iraki.
Bayanin ya kara da cewa taron zai mayar da hankali wajen bayyana muhimman abubuwa da ya kamata musulmi ya sani kan koyarwar kur'ani mai tsarki dangane da rayuwa ta zamantakewa.
Masana da dama daga kasar Iran da kuma kasar Iraki gami da malaman jami'oi ne za su halarci zaman taron, tare da gabatar da jabai da kuma kaddamar da makaloli.
626583