Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Plastineonline an bayyana cewa, kungiyar gwagwarmayar palastinawa ta jihad islami ta fitar da wani bayani da a cikinsa take cewa, .wagwarmaya ita kadai ce hanyar wanzur al'ummar musulmi cikin izza a irin wannan yanayi da musulmi suka samu kansu cikin zalunci da danniyar kasashe 'yan mulkin mallaka da kuma yahudawan sahyuniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa gwagwarmayar musulmi da larabawa ta tabbatar da cewa babu wata sauran dubara da tarage ma musulmi da larabawa illa bin tafarkin fito na fito da zaluncin 'yan mulkin mallaka.
Daga cikin misalin hakan har da gwagwarmayar da al'ummar lababan karkashin jagorancin hizbullah suke yi, da kuma gwagwarmayar kungiyoyin palastinawa, wanda hakan ya hana yahudawan sahyuniya cimma burinsu a cikin wadannan kasashe.
626564