IQNA

An Nuna Damuwa Kan Kyamar Musulmi A Kasar Holland

20:39 - August 05, 2010
Lambar Labari: 1967705
Bangaren kasa da kasa; Wani jami'in diplomasiyar kasar Turkiya a birnin Hague na kasar Holland ya nuna matukar damurwa kan yadda kyamar musulmi d aaddinin musulunci ke ci gaba da karuwa a kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na haberoku an bayyana cewa, wani jami'in diplomasiyar kasar Turkiya a birnin Hague na kasar Holland ya nuna matukar damurwa kan yadda kyamar musulmi d aaddinin musulunci ke ci gaba da karuwa a kasar ta Holland.

Jami'in ya ci gaba da cewa bisa la'akari da cewa al'ummar musulmi su ne marassa rinjaye a kasar Holland idan aka kwatanta da mabiya addinin kirista wadanda su ne suka fiyawa, wasu daga cikin kiristoci masu tsatsauran ra'ayi suna nuna wa musulmi wariya da kyama kai tsaye.

Ya ce abin bakin ciki ne manyan kasashe da suke da'awar kare hakkokin dan adam su zuba ido suna kallon yadda ake zarafin wasu mutane saboda kawai su ne marassa rinjaye a cikin wadannan kasashe.

Wasu suna danganta hakan da wadanda suka tasirantu da surutan mutumin dan kasar Holland da ke neman yin suna a duniya amma da sunan mai tsananin gaba da addinin musulunci.

626438

captcha