Bangaren kasa da kasa;a kasar Beljuim ne za a gudanar da kasuwar farko ta kasuwar baje kolin littafan Musulunci da cibiyar Musulunci ta tauhidi ta shirya a garin Liege
.
Kamfanin dillancin labarai da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga markazattawhid.e ta watsa rahoton cewa; a kasar Beljuim ne za a gudanar da kasuwar farko ta kasuwar baje kolin littafan Musulunci da cibiyar Musulunci ta tauhidi ta shirya a garin Liege. A wannan kasuwar baje kolin za a samu halartar marubuta musulmi a kasar ta Beljuim da inda suka baje kolin littafai a gurin wannan kasuwar baje kolin da ta samu karbuwa da jinjinawa matuka gaya.
627468