Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na tatar-informatin a shafin yanar gizo an bayyana cewa, za a bude wata babbar cibiyar nazarin ilmomin musulunci a kasar Mangolia, da take da dangantaka da babbar kwalijin bincike ilmomi ta kasar tare da hadin gwiwar wasu cibiyoyin musulunci.
Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin muhimman bangarorin da ayyukan nazarin za su mayar da hankali kansu akwai tarihin musulunci, akida da kuma muhimman ayyukan da aka aiwatar a cikin daulolin musulunci domin amfanin dan adam.
Yanzu haka dai akwai cibiyoyin musulunci na ciki da wajen kasar da suka sha alwashin bayar da gagarumin taimako domin aiwatar da wannan shiri, wanda masana daga sassa daban-daban na kasar za su shiga.
627533