Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo info-islam cewa babbar majalisar malaman addinin muslunci ta yankin kwarya-kwaryan cin gishin kai na Tataria na kasar Rasha ta bayyana ranar laraba mai zuwa a matsayin ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma mai zuwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa majalisar ta sanar da hakan ne sakamakon tattara bayanai na ilmin falaki da ke tabbatar da cewa ranar laraba za ta zama rana tafarko a watan Ramadan mai alfarma, a kan haka ta sanar da wannan rana a matsayin ta farkon Ramadan.
627521