Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tasahar sadarwa ta rasid cewa, za a gudanar da taron cika kwanaki arba'in da rasuwar bababn malamin addinin muslunci na kasar Labanan marigayi Allamah Sayyid Muhammad Hussain Fadlollah a garin Katif na kasar Saudiyya, wanda mabiya tafrakin iyalan gidan manzon Allah na yankin suka shirya gudanarwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa kwamitin marubuta na ashabul kalam shi ne ya shirya gudanar da zaman taron, wanda zai samu halartar malamai dam asana da kuma marubuta, inda za a gudanar da jawabai kan irin rawar da Allamah Fadlollah ya taka a bangarori daban-daban na ci gaban al'ummar musulmi a lokacin rayuwarsa.
Allamah sayyid Muhammad Hussain Fadlollah ya rasu ne a karshen watan Yunin da ya gabata, yana da shekaru 73 a duniya, inda aka gudanar da janazarsa a birnin Beirut fadar mulkin kasar Labanan.
628095