IQNA

An Kirayi Musulmin Birtaniya Da Kada Su Sayi Dabinon Isra'ila

23:23 - August 09, 2010
Lambar Labari: 1970235
Bangaren kasa da kasa; Wata kungiya farar hula a birnin Lester na kasar Birtaniya ta bukaci al'ummar muslmin kasar da kad asu sayi dabinon da ake kawo daga haramtacciyar kasar Isra'ila.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na twoarticles na yanar gizo cewa, wata kungiya farar hula a birnin Lester na kasar Birtaniya ta bukaci al'ummar muslmin kasar da kad asu sayi dabinon da ake kawo daga haramtacciyar kasar Isra'ila zuwa kasar ta Birtaniya.

Bayanin ya kara da cewa wannan kungiya da ba ta ta da wata dangantaka da gwamnati, ta dauki wannan mataki ne domin masaniyar da take da ita kan cewa musulmin kasar suna yin amfani da dabino a lokacin azumin ramadan.

Kungiyar ta ce bisa la'akari da cin zarafin dan adam da haramtacciyar kasar isra'ila ke yi a yankunan da ta mamaye mallakin palastinawa, tana fatan musulmi za su taimaka wajen kaurace ma dabinonta.

629083
captcha