IQNA

Tarjamar Kur'ani Karo Na Goma Sha Bakwai A Birtaniya

16:20 - August 10, 2010
Lambar Labari: 1970836
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da aikin tarjamar kur'ani mai tsarki a cikin harshen turanci da ya fi girma wanda shi ne irinsa na farko a tarihin kasar, wanda ka saka a cikin kayyakin da za a nuna a baje kolin littafan Musulunci a kasar a cikin wannan wata mai alfarma.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantaw da ta hada shi da malam Rahim Daulti shugaban baje kolin littafai na Qods razavi ya bayyana cewa, an gudanar da aikin tarjamar kur'ani mai tsarki a cikin harshen turanci da ya fi girma wanda shi ne irinsa na farko a tarihin kasar, wanda ka saka a cikin kayyakin da za a nuna a baje kolin littafan Musulunci a kasar a cikin wannan wata mai alfarma na ramadan.

Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu an kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da wannan baje koli da za a nuna wannan kur'ani da sauran littafai da aka tarjama a cikin harshen turanci a kasar ta Birtaniya.

Kur'anin an rubuta shi ne a kan manyan takardu, da kuma manyan haruffa, wanda hakan ya san shi ya zama mai nauyi da ya kai kilo 46, fadinsa kuma santi mita hamsin a cikin saba'in.

630028





captcha