IQNA

An Nuna Hotunan Dadadden Kur'anin China A Baje Kolin Kur'ani

16:20 - August 10, 2010
Lambar Labari: 1970837
Bangaren kasa da kasa; A bangaren da aka kebe wa jami'ar Al-mostafa a baje kolin kur'ani na duniya da ake gudanarwa a birnin Tehran, daliban kasar China sun zo da hotunan wani dadaden kur'ani mai tsarki da ke kasar da ake lissafa shi a cikin kayyakin tarhi dadaddu.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, mai aiko masa da rahotanni daga wurin gudanar da kasuwar baje kolin kayyakin kur'ni a birnin Tehran ya habarta cewa, a bangaren da aka kebe wa jami'ar Al-mostafa a baje kolin kur'ani na duniya da ake gudanarwa a birnin Tehran, daliban kasar China sun zo da hotunan wani dadaden kur'ani mai tsarki da ke kasar da ake lissafa shi a cikin kayyakin tarhi dadaddu da kasar take mallaka.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan kur'ani mai tsarki ya kunshi dukkanin surori daga bakara zuwa nasi, amma rubuta su ne acikin babbar warka da kanan rubutu.

Tsawon warkar da aka rubuta kur'anin ta kai mita 650, yayin da fadinta ya kai mita tara a kwance. A gefen kur'ani an rubuta wasu abubuwa na ilimin larabci.

629935

captcha