IQNA

An Nuna Tafsiran Kur'ani Na Sunna Da Shi'a A Baje Kolin Kur'ani

17:49 - August 10, 2010
Lambar Labari: 1970911
Bangaren kasa da kasa; An nuna wasu daga littafan tafsiri na sunna da shi'a a taron baje kolin kur'ani da ake gudanarwa a birnin Tehran, wadanda a ka tarjama acikin harshen urdu, a dakin jami'ar Al-mostafa a bangaren daliban kasar Pakistan.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an nuna wasu daga littafan tafsiri na sunna da shi'a a taron baje kolin kur'ani da ake gudanarwa a birnin Tehran, wadanda a ka tarjama acikin harshen urdu, a dakin jami'ar Al-mostafa a bangaren daliban kasar Pakistan da suka halarci gasar domin nuna liffan addini da aka rubuta ko tarjama a cikin harshen Urdu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa. Wannan baje koli na kayyakin kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Tehran, ya sha banban da na sauran shekarun da suka gabata.

Daga cikin abubuwan da aka nuna a wannan karon akwai wasu littafai na addini da aka tarjama a cikin wasu harsuna, wanda hakan ya mayar da ita ta kasa da kasa.

629890




captcha