IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Kyautata Rubutun Kur'ani A Madina

17:49 - August 10, 2010
Lambar Labari: 1970912
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da zaman taro kan kyautata rubutun kur'ani mai tsarki a birnin Madina mai alfarma da zai samu halartar marubuta daga sassa daban-daban na duniyar musulmi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alriadh cewa, za a gudanar da zaman taro kan kyautata rubutun kur'ani mai tsarki a birnin Madina mai alfarma da zai samu halartar marubuta daga sassa daban-daban na duniyar musulmi da ma wasu kasashe da ba na musulmi ba.

Taron zai dubi ne kan muhimmancin kyautata rubutun kur'ani mai tsarki da kuma kwadaitar da marubuta kan hakan. Bayan nan kuma za a gudanar da laccoci.

Bayanin ya ce a lokacin da za a kammala zaman taron za a zabi wasu daga cikin rubuce-rubucen da suka fi kayatarwa domin ba su kyautuka.

629814
captcha