Bangaren kasa da kasa; An bude wani sabon shafin yanar gizo na khatmar kur'ani mai tsarki da ya kebanci watan Ramadan mai alfarma a kasar Turkiya, wanda zai rika watsa karatun kur'ani kai tsaye sa'oi ashin da hudu a kowace rana.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na ortakhatim cewa, an bude wani sabon shafin yanar gizo na khatmar kur'ani mai tsarki da ya kebanci watan Ramadan mai alfarma a kasar Turkiya, wanda zai rika watsa karatun kur'ani kai tsaye sa'oi ashin da hudu a kowace rana a cikin watan mai alfarma.
Bayanin ya kara da cewa a cikin karatukan da za a rika sanyawa a shafin har da na manyan malamai da fitattun makaranta kur'ani mai tsarki da suka shahara a duniya.
Ga masu bukatar sauraren karatun kur'ani mai tsarki a salon karatu na tartili suna iya komawa domin duba shafin. Cibiyar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) suka shirya wannan shafi.
629818