IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Kayayyakin Halal A Kasar Jamus

17:50 - August 10, 2010
Lambar Labari: 1970914
Bangaren kasa da kasa; A mako mai zuwa ne za a gudanar da wani taro na kayayyakin halal a addinin muslunci a kasar Jamus, wanda wata cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin Doseldrov na kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na world poultry na yanar gizo cewa, a mako mai zuwa ne za a gudanar da wani taro na kayayyakin halal a addinin muslunci a kasar Jamus, wanda wata cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin Doseldrov na kasar ta Jamus.

Bayanin ya ci gaba wannan taro zai samu halartar masana musulmi da ma wasu da aka gayyata daga wasu garuruwa na kasar domin gane wa idanunsu yadda taron zai gudana.

Babbar manufar gudanar da wannan taro dai ita ce tantance kayayyakin abinci na halal da mulmi suke yin amfani da su daidai da yadda addininsu ya umurta, da kuma kaurace wa ababe na abinci da aka haramta.

629721

captcha