Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar kula da harkokin ala'du da bunsa ilimi cewa, shugaban cibiyar kula da harkokin al'adu da bunkasa ilmomin addinin muslunci ta kasar Iran Mahdi Mostafavi zai gudanar da wani zaman taron manema labarai domin bayyana musu matsayin cibiyarsa kan harkoki na kasa da kasa da kuma dangantakarsu.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro zai yi tsokaci kan muhimman batutuwa da ya kamata kafofin yada labarai su samu cikakkiyarv masaniya kansu dangane da ayyukan da cibiyar take gudanarwa a matsayi na kasa da kasa.
Haka nan kuma taron manema labaran yana da muhimmanci ga manema labarai, inda za a ba su surar ayyukan cibiyar dangane da ayyuaknta na bai daya.
629601