IQNA

Musulmi Ba Su Da Bayani Kan Ayyukan Kur'ani A Senegal

18:34 - August 10, 2010
Lambar Labari: 1970925
Bangaren kasa da kasa; Malaman kasar Senegal sun taka gagarumar rawa a fagen kur'ani mai tsarki ta hanayar rubuta shi da koyo gami da koyar da ilmominsa, amma saboda matsaloli na rashin hanyaoyon isar da hakan ga sauran al'ummomi duniya bat a labarin haka.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, daya daga cikin daliban addinin muslunci da ke karatu a reshen falsafar Musulunci a jami'ar Al-mostafa da ke birnin Qom kuma dan asalin kasar Senegal Dawud Tal Sidi, ya bayyana cewa malaman kasar Senegal sun taka gagarumar rawa a fagen kur'ani mai tsarki ta hanayar rubuta shi da koyo gami da koyar da ilmominsa, amma saboda matsaloli na rashin hanyaoyon isar da hakan ga sauran al'ummomi duniya bat a labarin irin wannan gagarumin aiki.

Ya ci gaba da cewa yanzu haka dubban kur'anai da manyan malaman addinin muslunci da suka gabata suka rubuta kuma ana ci gaba da ajiye su a gidajen tarihi na kasar.

Bugu da kari ma akwai littafai da aka rubuta a bangarori daban-daban na addinin muslunci tun tsawon daruruwan shekaru da suka gabata, amma mafi yawan al'ummomin duniya ba su da labarin hakan.

629216





captcha