Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a ci gaba da gudanar da taron baje kolin kur'ani mai tsarki da ake yi a birnin Tehran an nuna wani kur'ani mai suna kur'anin atlas a bangaren da aka ajiye littafan da aka tarjama da harshen turkanci da suke da dangataka da ilmomin kur'ani da aka kawo su a wurin baje kolin.
Bayanin ya ci gaba da cewa bangaren da aka ajiye kayayyakin harshen turkanci na jami'ar Al-mostafa (SAW) na daga cikin bangarorin da suka dauki hankula a wurin.
Baya ga littafin kur'anin atlas da shahararren marubucin nan Ahmad Badir ya rubuta, an fitar da wasu daga cikin littafan addinin muslunci da aka rubuta ko tarjama a cikin wannna harshe.
630773