IQNA

Za A Gudanar Da Makon Nahjul-Balagha A Kasashe Hudu

15:46 - August 11, 2010
Lambar Labari: 1970990
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da tarukan makon nahjul balagha a kasashe hudu na duniya, wanda cibiyar kula da bunkasa harkokin al'adu da ilimi ta dauki nauyin shiryawa da kuma gudanarwa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Mostafa Safavi mataimakin shugaban kasa kan harkokin al'adu a wani taron manema labarai ya bayyana cewa, za a gudanar da tarukan makon nahjul balagha a kasashe hudu na duniya, wanda cibiyar kula da bunkasa harkokin al'adu da ilimi ta dauki nauyin shiryawa da kuma gudanarwa nan ba da jimawa ba.

A taron manema labaran da aka gudanar yau Mostafavi ya bayyana cewa hakika gudanar da irin wannan taro kan nahjul balagha yana da matukar muhimmanci a wannan lokaci.

Ya kara da cewa ilimin Imam Ali (AS) ilimi ne da dukkanin 'yan adam, wanda ya zama wajibi a watsa shi a duniya domin dora bil adama kan sahihin tunani na rayuwa.

630665







captcha