IQNA

Taron Raya Tunanin Musulunci A Birnin Alkahira

15:45 - August 11, 2010
Lambar Labari: 1970991
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da wani zaman taro a birnin Alkahira na kasar Masar da zai yi dubi kan hanyoyin raya mahangar addinin muslunci kan zamantakewar jama'a da za a fara gudanarwa a rana ta biyu a cikin watan Ramadan mai alfarma.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga kamfanin dillancin labarai na mohit a shafinsa na yanar gizo an bayyana cewa, za a fara gudanar da wani zaman taro a birnin Alkahira na kasar Masar da zai yi dubi kan hanyoyin raya mahangar addinin muslunci kan zamantakewar jama'a da za a fara gudanarwa a rana ta biyu a cikin watan Ramadan.

Rahoton ya ci gaba da cewa babban kwamitin kula da harkokin addinin Musulunci na kasar ne zai dauki nauyin shiryawa da gudanar da wannan zaman taro, da zai samu halartar fitattun malaman addini na kasar.

Daga cikin malaman da za su halarci taron akwai babban mai bayar da fatawa na jami'ar azhar sheikh Ahmad Tayyib, sai kuma Mahmud Hamdi ministan ma'aikatar kula da harkokin addin ta kasar.

630677




captcha