IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Hadaddiyar Daular Larabawa

15:45 - August 11, 2010
Lambar Labari: 1970992
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta kasar hadaddiyar daular larabawa da aka yi wa lakabi da allaziz, wadda ta kebanci watan Ramadan mai alfarma, da za a gudanar a birnin Sharja na kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a wani labari da ya nakalto daga jaridar darulkhalij an habarta cewa, za a gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta kasar hadaddiyar daular larabawa da aka yi wa lakabi da allaziz, wadda ta kebanci watan Ramadan mai alfarma, da za a gudanar a birnin Sharja na kasar ta hadaddiyar daular larabawa.

Wannan gasa dai cibiyar kula da harkokin kur'ani ta kasar ce ta shirya ta tare da hadin gwiwa da cibiyar raya a'adu da motsa jiki ta laziz da ke birnin Sharjah.

Kasem Muhammad Fadil daya daga cikin masu sanya ido kan shirye-shiryen gasar ya bayyana cewa yanzu haka sama da makarnat 150 daga cikin makarantar kasar suka rijistar shiga gasar.

630666


captcha